<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ni Mai Laifi Ɓatacce LW164</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ni mai laifi ƃatacce,
 Jininka kaɗai ya isa.
 Zunubaina sun yi yawa,
 Jininka kaɗai ya isa

[V2]
 Yesu !  ga ni wurinka!
 Ceto na ke nema.
 Dauɗar zuciya, laifina,
 Jininka kaɗai ya isa .

[V3]
 2) Muryarka na riƙa ji,
 &quot;Jinina na bayar don ceto,&quot;
 Amsa na ke so in yi,
 Duk na rasa ikon roƙo,

[V4]
 Yesu! ga ni wurinka !
 Ceto na ke nema.
 Muryarka ta ce da ni,
 &quot;Jinina na bayar don ceto.&quot;

[V5]
 3) Nan na tsaya ƃaratacce,
 Jininka kaɗai ya isa.
 Ni yanzu ka tsarkake.
 Jininka kaɗai ya isa.

[V6]
 Yesu! ga ni wurinka!
 Tsarki na ke nema.
 Ranka cikina kaɗai
 Za ya isa mini ceto.

[V7]
 4) Bawanka na zama yau,
 Jininka kaɗai ya saye ni,
 Aikinka kaɗai in yi,
 Ni ne naka, ka cece ni.

[V8]
 Yesu! ga ni wurinka!
 Manzonka ka aika.
 Jininka mai fansata,
 Jininka kaɗai ya isa.</lyrics>
<hymn_number>164</hymn_number>
</song>